Mutum 5 da Arzikinsu yafi kasafin kudin Nigeria
Wani rahoton da kungiyar agaji ta Oxform ta fitar ya bayyana irin mummunar tazarar da ke tsakanin masu kudi da talakawa a yankin Afirka ta Yamma.
.
Rahoton ya ce masu kudin yankin guda 10 sun fi kasashe 16 na yankin arziki. .
Oxform ta ce kasashen Afirka ta Yammar na asarar akalla dala biliyan 9.6 a kowacce shekara ta hanyar dage haraji ga kamfanonin kasashen duniya.
.
Irin wadannan kudaden, in ji rahoton, za a iya amfani da su wajen gina asibitocin zamani guda 100 a kowace shekara a yankin.
.
Najeriya ce ta fi kowacce kasa arzikin man fetur a Afirka, amma 'yan kasar da dama na fama da zazzafan talauci, wanda ake alakantawa da cin hanci da rashawa da rashin adalcin shugabanni.
.
Masu arzikin Najeriya
Rahoton Oxform ya ce mutum biyar masu arzikin Najeriya da arzikin nasu ya kai dala biliyan 29.9, ya yi wa kasafin kudin kasar na shekarar 2017 shal wanda ya kama naira tiriliyan 7.29, kwatankwacin dala biliyan 23.97.
.
Jaridar Forbes ta wallafa sunayen mutum biyar 'yan Najeriyar da suka fi arziki a kasar kamar haka:
Aliko Dangote
Mike Adenuga
Abdul Samad Rabiu
Folorunsho Alakija
Femi Otedola
#BBCNews #BBCHausa

ABOUT AREWAONEHello ArewaOne Is Welcome You To The Fantastic Website In Northern Nigeria, ArewaOne.com.ng Is Starting Published Articles Sound,Videos And Good Content.
Newer Posts
Newer Posts
Older Posts
Older Posts
Comments