Featured Post

Jim kadan bayan Barcelona ta bayyana daukar Griezmann a ranar Juma'a, Atletico Madrid ta mayar da martani da cewa kudin da Barcelona ta biya ya yi kadan.

Jim kadan bayan Barcelona ta bayyana daukar Griezmann a ranar Juma'a, Atletico Madrid ta mayar da martani da cewa kudin da Barcelona ta biya ya yi kadan.

Kulob din ya ce yuro miliyan 200 ne ya kamata Barcelona ta biya a matsayin kudin da yake cikin yarjejeniyarsa idan wata kungiya na son sayansa kafin kwantaraginsa ya kare.

Barcelona ta biya yuro miliyan 120 ne kan dan wasan, wanda a da yake a matsayin yuro miliyan 200 a lokacin da aka fara tattaunawa, in ji Atletico.

A ranar 1 ga watan Yuli ne dai aka rage farashin dan wasan daga yuro miliyan 200 zuwa 120. "Mun yi imanin cewa kudin da aka biya bai cika ba domin kuwa an rufe tattaunawa da Barcelona kafin a rage farashin dan kwallon daga yuro miliyan 200 zuwa 120," in ji kulob din.

Dan wasan mai shekara 28 wanda ya lashe kofin duniya, ya kulla yarjejeniyar shekara biyar ciki har da Yuro miliyan 800 kudin da wata kungiya za ta dauke shi kafin yarjejeniyarsa ta kare. #atleticomadrid #barcelona
ABOUT AREWAONEHello ArewaOne Is Welcome You To The Fantastic Website In Northern Nigeria, ArewaOne.com.ng Is Starting Published Articles Sound,Videos And Good Content.
Newer Posts Newer Posts Older Posts Older Posts

More posts

Comments

Post a Comment