Featured Post

An Tabbatar da Tanko Muhammad a Matsayin Alkalin Alkalan Nigeria

MAJALISAR DATTAWA TA TABBATAR DA TANKO MOHAMMED A MATSAYIN ALKALIN ALKALAN NIJERIYA

Daga Rilwanu Labashu Yayari

Shugaba Buhari ya nada Alkali Tanko Mohammed a watan Junairu bayan dakatar da tsohon Alkalin alkalai, Walter Onnoghen, wanda aka tuhuma da zargin boye kadarorinsa.

An haifi mai Shari'a Tanko a ranar 31 ga Disamba, 1953 a Doguwa, karamar hukumar Giade ta jihar Bauchi.

Ya halarci makarantar gwamnatin Azare inda ya yi karatun sakandare kuma ya kammala a shekarar 1973, sannan ya karasa jami'ar Ahmadu Bello inda ya yi karatun Digir.

Daga baya ya yi karatun Majistir a 1984 da Doktora a jami'ar Ahmadu Bello a shekarar 1998
ABOUT AREWAONEHello ArewaOne Is Welcome You To The Fantastic Website In Northern Nigeria, ArewaOne.com.ng Is Starting Published Articles Sound,Videos And Good Content.
Newer Posts Newer Posts Older Posts Older Posts

More posts

Comments

Post a Comment