Featured Post

Kannywood : Marayun’ Da Adam Zango Ya Bari A Garin Kaduna Sun Koka Bisa Komawarsa Kano

Kaurar da fitaccen jarumin finafinai Hausa na Kannywood, wato Adam A. Zango, ya yi daga garin Kaduna zuwa birnin Kano ta girgiza rayuwar wasu matasa da su ka kasance tare da shi a lokacin da ya ke a Garin Gwamna, inda har su ka kira kansu da “marayu a halin da mu ke ciki yanzu”. 


Bayanin hakan ya fito ne daga bakin wadannan matasa, wadanda su ka bukaci a sakaya sunansu. Bayanai sun nuna cewa, jarumin ya koma Kano da zama, inda yanzu sai jifa-jifa ya ke shiga garin Kaduna, garin da ya ke da yara matasa masu dimbin yawa da ke bibiyar sa. Matasan sun shaida wa LEADERSHIP A YAU LAHADI cewa, tun bayan da jarumin ya bar Kaduna a cikin shekarar da ta gabata, wato 2018, ya koma Kano, su ke fuskantar matsin rayuwa da kunci da fatara, domin a lakacin da kwararren jarumin ya ke zaune a garin su na iya samu wadatar rayuwa ta hanyarsa, saboda taimakon su da ya ke yi ta hanyoyi daban-daban. 

A yayin da wakilinmu ya tambaye su irin hanyoyin da Jarumi Zango ya ke taimaka mu su da ita, sai aya daga cikinsu ya ka da baki ya ce, “Adam Zango mutum ne mai kyauta da kuma tausayi. Idan ma bai dauki kyauta ya ba ka hannu da hannu ba, to zai ba ka aikin da za ka samu abinda za ka samu ka rike kanka ko kuma saka ka a wata harka, wacce za ka karu.” Daya matashin kuma ya kara da cewa, “a lokacin Maigida Adam ya ke garin nan na Kaduna wallahi hatta iyayena na fi iya taimakon su, saboda karuwar da mu ke yi da shi. Shi ya sa kullum su ke yi ma sa addu’a. 

“Shi fa mutum ne wanda bai san ka ba, amma sai ya taimake ka. Wallahi ni dai ba wani sanina ya yi sosai ba, amma a dalilinsa na iya rike kaina. Kawai ya ga kullum sai na je inda ya ke ne, shi ne ya ce a rika ba mu aikin da za mu rike kanmu. “A wasu lokutan aike-aike kawai na ke yi zuwa gurare, amma sai ka ga na dan samu abinda zan rike kaina. Yanzu kuwa komai ya tsaya.” Wakilinmu ya tambaye su shin a yanzu ko wane kira su ke da shi ga jarumin, sai daya daga cikinsu ya ka da baki ya ce, “ya taimaka kawai ya dawo Kaduna da zama, domin ya bar marayu a nan.” Binciken wakilinmu ya nuna cewa, da alama tuni dai jarumin ya yi wa Birnin Dabo shigar da babu tashi, domin har ya saye gidan da ke kusa da gidan da ya kama haya zai gyara shi ya koma, wanda hakan ke nuni da cewa, bai shirya barin Kinkimin Gari Mai Dala Da Gwauron Dutse ba. 

Da ma dai yawancin manyan jaruman Kannywood su kan tara yara a karkashinsu, wadanda su ke mafi yawansu su na dogara da su ne wajen ci da sha da sutura da taimakon iyayensu, kamar yadda a ka jarumai irin su Sani Danja, Ali Nuhu, Yakubu Mohammed, da sauransu kullum su ke kewaye da mabiya. Hatta tsofaffin jarumai irin su Hamisu Iyantama, Ibrahim Mandawari da makamantansu an ci irin wannan kasuwa a karkashinsu a shekarun baya, inda za ka rika ganin ofisoshinsu cike da matasa; wasu sun san su, wasu ma ba su san su, illa dai kawai idan abin taimako ya kama, sai a yi dukkansu su amfana. Wasu daga cikin irin wadannan matasan su kan samu damar shiga makarantu su samu ilimi na zamani. 

shi dai Adam Zango ya fara yin shuhura ne a Kano, amma tun bayan da a ka yi Badakalar Hiyana har hukumar tace finafinai ta jihar Kano a karkashin jagorancin Abubakar Rabo ta kama shi ta tura kurkuku, sai ya yi kaura daga Kano a wajejen shekarar 2008 ya koma Kaduna. A can garin Kadunan ne furodusoshin Kano su ka rika takakkiya su na zuwa su na shirya ma sa finafanai har ya samu cikakkiyar daukaka, farin jini da karbuwa a cikin finafinan Hausa. 

Daga dukkan alamu kura ta lafa a Kano bayan fiye da shekara goma ’yan fin din Hausa su na samun tsangwama daga waccan hukumar tace finafinai. Don haka ba abin mamaki ba ne don an ga Jarumi Zango ya dawo garin da ya fara tofo. 

A yanzu dai za a zura idanu ne a ga ko zai sake koma wa Kaduna saboda koken wadancan ‘marayu’ da ya bari ko kuma zai tsaya a Kano ya sake kafa wani sansanin ne. Lokaci shi ne zai tabbatar.

Leadershipayau.
ABOUT AREWAONEHello ArewaOne Is Welcome You To The Fantastic Website In Northern Nigeria, ArewaOne.com.ng Is Starting Published Articles Sound,Videos And Good Content.
Newer Posts Newer Posts Older Posts Older Posts

More posts

Comments

Post a Comment